WASIKAR GARGADIN AMURKA GA IRAN MI TA KUNSA?Siddiq Ahmad
WASIKAR GARGADIN AMURKA GA IRAN MI TA KUNSA?
Hukumar Shugaban kasar Amurka Biden ta tura wasikar gargadi ga Iran a watan da ya gabata dangane da ayyukan da kasar ke gudanarwa ta hanyar fadada manufofinta musamman batun mallakar makamin Nukiya.
A wasikar kusoshin Gwamnatin Amurka da Isra'ila sun yi gargadin cewa Iran ta kebanci wadansu Malamai masu hazaka da za su jibinci lamarin samar da makamin Nukiya.A cewarsu kasar ta Iran za ta yi amfani da shagalar da Amurka din take yi a kan lamuran zabe domin samar da makamin Nukiliya din a cewarsu.
Hukumomin leken asirin Amurka da Isra'ila da manyan 'yan siyasar kasashen biyu sun dukufa sosai wajen riska da bibiyar aikin Iran,musamman yadda Hakan zai karawa Shugaban Addinin kasar Ayatullahi Khamne'i daukaka da karbuwa a cikin kasar da wajenta.
Kafar yada labaran CNN sun bayyana yadda CIA suka gano wani yunkurin Iran na KASHE tsohon Shugaban qasar Amurka Donald trumps banda Wanda ya faru a satin da ya gabata.
Wani kusa a cikin Gwamnatin Biden ya bayyana cewa:"Hakika wasikar da Amurka ta turawa Iran tana da matukar tasiri,duk da haka Muna matukar bibiyar ayyukan Iran dangane da samar da makamin Nukiliya".
No comments: