SAYYID KHAMENE'I YA RANTSAR DA SABON ZABABBEN SHUGABAN IRAN. Bilya Hamza Dass

SAYYID KHAMENE'I YA RANTSAR DA SABON ZABABBEN SHUGABAN IRAN
Bilya Hamza Dass
 

A Hukumance yau Syd Khamene'i ya rantsar da sabon shugaban Iran Dr. Mas'ud Pezeshkian ya sanya albarka ya bashi takardan fara ayyukan ƙasa da al'umma daga yau. 

Taron wanda akayi shi a Husainiyar Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran, cikin manyan baƙi da suka halarta harda tsofin shugabanin ƙasar Mr. Hassan Rauhani da Shaikh Sayyd Muhammad Khatami.

Manyan baƙi ne suka halarci taron daga ƙasashen duniya daban-daban da wakilan gwamnati. Cikin jawabin da ya gabatar yace aikin gwamnati na farko shi ne inganta rayuwar ƴan ƙasa, ya kuma nemi jami'an gwamnati su inganta alaƙa da kasashen waje.

Syd Khamene'i' wanda shine Jagoran ƙasar mafi daɗewa zuwa yanzu, ya rantsar da mutane  shida a jere matsayin shugabannin ƙasa a lokaci daban-daban tun daga Rafsanjani.

Shugabannin ƙasa da Syd Ibrahim ya rantsar cikin shekaru 35 yana Jagoran ƙasar 

1. Akbar Hashemi Rafsanjani (1989-1997) 

2. Mohammad Khatami (1997-2005)

3. Mahmoud Ahmadinejad (2005-2013) 

4. Hassan Rouhani (2013-2021)

5. Ebrahim Raisi (2021) 

6. Dr. Mas'ud Pezeshkian (2024)

—Bilya Hamza Dass

No comments:

Powered by Blogger.