Shaikh Zakzaky:Tauraron Afrika!Daga Yusuf Kabir kabiruyusuf533@gmail.com.07081351143
Shaikh Zakzaky:Tauraron Afrika!
Daga Yusuf Kabir
kabiruyusuf533@gmail.com.07081351143
Sunnar Allah ce sai ya jarabi bayinsa sannan ya daukaka darajarsu.Annabi Yusuf (as) an raba shi da Mahaifinsa tsawon shekaru don cancantar da shi ga daraja mai girma.
Annabi Ibrahim (as) sai da aka wurga shi wuta,aka tunkudo masa dangogin jarabawa/Musibu sannan ya taka matsayin da ya kai na daukaka.
Sad da Imamu Husaini (as) zai bar garin Madina ya yi mafarki da Manzon Allah (s) yace da shi:"Ya Husaini! ka na da wata daraja a wajen Allah ba za ka same ta ba sai ka zamanto Shahidi."
Hakika Allah ya jarabi Shaikh Zakzaky (h) da dangogin musibu (da za a iya cika manyan Littafai wajen nazartar su da sharhinsu) sannan yake samun matsayin da yake samu.Imam Sadiq (as) Yana cewa:"Hakika manya-manyan darajoji na tare da manya-manyan bala'oi.Allah bai taba son wasu mutane ba face sai da jarabe su."
Jagoranmu bai ya tsaya kyam kamar tsaunin Everest, tabbas Allama mutum ne na musamman domin aikin musamman.
Imam Mahdi (af) Yana cewa:"Akwai tutar wilaya za ta zo daga yammacin Duniya."(Littafin asaruz-Zuhur na Ayatullahi Kaurani volume 2).
No comments: