HUJJOJIN JUYAYIN ASHURA DAGA MANZON ALLAH (S)
HUJJOJIN JUYAYIN ASHURA DAGA MANZON ALLAH (S)
10. Manzon Allah (s) yana cewa akan Hasan da Husaini: "Hakika su ruhin raina ne masu faranta mini: "(Sahihul bukari kitabul adab)
11. Manzon Allah (s) yana cewa: "Hakika Hasan da Husaini sune farin ciki na a wannan al'ummar”.(Kasa'isul nisa'i page 37).
12. Manzon Allah (s) yana cewa: "Ya Allah! ka sani hakika Hasan da Husaini 'yan Aljanna ne”.(Littafin Zaka'irul Ukba page 130).
14. Manzon Allah (s) yana cewa: "wanda yake so na to ya so wadannan biyun (sai ya nuna Hasan da Husaini) (Sunanil baihaki vol 2, page 263).
15. Manzon Allah (s) yana cewa: "Ya Allah ka shaida Ina son su, ka so su, ka so wanda yake son su”. (Kanzul Ummal vol 7, page 107)
16. Manzon Allah (s) yana cewa: "Hasan da Husaini Shuwagabanni samarin Aljanna ne”.(Tirmiziy vol 2, page 306).
17. Manzon Allah (s) yana cewa: "Hasan da Husaini su ne Shuwagabannin samarin aljanna, amma Mahaifinsu ya fi su matsayi”. (Ibn Majah babin falalar Sahabbai).
No comments: