Khalil:saurayin da ya nemi Mahaifiyarsa ta kawo masa kafafunsa domin ya yi bakwana da su a Gazza.

Khalil:saurayin da ya nemi Mahaifiyarsa ta kawo masa kafafunsa domin ya yi bakwana da su a Gazza.


Khalili Mikdad mai shekaru 47  Yana cikin Wanda harin kisan kisan kiyashin da Isra'ila ta kaddamar a Khan-Yunus ya rutsa da shi.Ya bayyana cewa:"Na kasance Ina dauke da  Kula wacce babu komai a cikinta daga  Tantunmu domin zuwa nemowa iyalina abinci.Kwatsam sai na ga yanayin sama ya canza,hasken Rana ya canza ya koma duhu,har na yi karamar Suma,na farfado na ga kafafuwana a cire,na yi kokarin yunkurawa Amma na kasa,har na manta ma cewa Ina tafiya a baya"

Khalil ya ci gaba da cewa,na nemi Dana da yake tare da ni na rasa,a yayin da kawai na ga wani yanki na tufafinsa."

Harin kisan kiyashin da Isra'ila ta kai a ranar 13/2024 da ta gabata a yankin Khan-Yunus ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa 90 da raunata 300 a lokaci guda.

Shugaban kasar Isra'ila Benjamin Natanyahu ya bayyana sun Kai harin ne domin halaka babban Kwamandan Kassam Muhammad Daifi,Wanda dakarun Hamas suka musa cewa harin ya rutsa da shi.

No comments:

Powered by Blogger.