Ba Alphanchi ba, ba Feminism ba.Moghniyya Ahmad.07081351143

Ba Alphanchi ba,  ba Feminism ba.
Moghniyya Ahmad.

Kalmar Alphanchi da Feminism kalmomi ne da ake amfani da su a social media musamman Facebook domin bayyana Jinsin maza a matsayin mugaye,ko bayyana Jinsin mata a matsayin azzalumai.
 A nan kuma,bai kamata mabiyin Iyalan Annabta (as) Sister/Brother su aminta da kalmomin nan guda biyu ba wato "Alphanchi" da Feminism" domin dukkaninsu sun sabawa koyarwar Limaman shiriya  (as).Sannan babu  abunda za su haifar sai kara hefa gaba  da kiyayya a tsakanin maza da mata.Da'awar Alphanchi  da ke Kiran rashin tausayawa Jinsin mata ko mata mugaye ne ba kuskure ce,haka  da'awar Feminism da ke kiran da nu na namiji mugu ne,ba-dan-goyo ba ne,ko shi buhun qaya ne,ko duk wacce ta riki namiji Uba za ta mutu marainiya ba haka ba ne;a kowanne jinsi akwai mutanen kirki da na banza,kamar mutum ne fa yace:"Ai duk 'Yan  Shi'a mutanen kirki ne,ko duk 'yan Izala marassa kirki ne,ko duk 'Yan Tijjaniyya mutanen kirki ne,kun ga wannan maganar ba za ta karbu ba a wajen mai hankali da nazari.
A kowanne jinsi a cikin kowacce firka  akwai mutanen kirki da na banza don haka,rikon Jinsi a matsayin madogara ba zai taba haifar da xa mai ido ba.

Hikimar Allah ce ya halicci maza da mata ya hada su a muhallin rayuwa domin su taimaka juna da yin rayuwa mai ma'ana.

Za mu ci gaba insha Allahu.

No comments:

Powered by Blogger.