SAYYID KHAMENE'I:MUTUMIN DA TSALLAKE HARIN KISA SAMA DA DUBU

 SAYYID KHAMENE'I:MUTUMIN DA TSALLAKE HARIN KISA SAMA DA DUBU
Wata cibiyar binciken tsaro tace, cikin shekaru 50 Syd Khamene'i ya tsallake shirin k!sa fiye da sau dubu ɗaya a lokaci daban-daban.

Cibiyar wacce ɗalibai masu ƙoƙarin neman kwarewa sukewa Jagoranci da asalin sunan ta be bayyana ba, tace yanzu haka Jagoran Addini na Iran yana cikin mutune mafi samun tsaro a duniya.

Lokacin da yake shugaban ƙasar Iran daga 1981 zuwa 1989 an kirkiri wasu kungiyoyin ta'@danci sama da 126 domin su ga bayan shi, amma hakan be yiyuwa ba. Rahoton yace, babu wani Mako (sati) daya taɓa wucewa ba tare da sun samar da wani sabon shiri ba.

An kashe Miliyoyin kuɗi masu yawa an tanada kayan ayyuka masu yawa domin ganin bayan shi amma ba'a yi nasara ba.

An raunata hannun daman Syd Ali Khamenei a wani harin bam da aka kai a shekarar 1981, lokacin yana shugaban kasar Iran. Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Yunin 1981, lokacin da wani bam ya tashi a wurin taron jam'iyyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Tehran.

Syd Khamenei ya samu munanan raunuka a hannunsa na dama, daga baya anyi masa ayyukan tiyata kuma ya samu lafiya. Harin ya kashe manyan wakilan gwamnatin Iran su 72, kuma wannan harin musaman saboda Syd Khamene'i a kayi shi.

Sai dai bayan Syd Khamene'i ya farka daga dogon suma da yayi yayi takaicin jin labarin cewa, harin ya kashe masa manyan abokan aiki da suka haɗa da;

Shaid Ayatullah Mohammad Beheshti, babban alkalin kasar Iran na farko bayan juyin musulunci. Shahid Mohammad Javad Bahonar, firaministan kasar Iran da wasu manyan jami'an gwamnati da malamai da dama sama da mutum 65. Kuma ƙungiyar MKE ne ta tsara harin a lokacin.

Yau shekarun Syd Khamene'i 85 a duniya. Duk wanda yayi kokarin ganin bayan shi sai ya tafi ya barshi, Shugabanin ƙasar Amurika 5 ne suka tafi suka wuce yana nan daram. Allah ya ƙara lafiya Jagora.

—Bilya Hamza Dass

No comments:

Powered by Blogger.