Adalci a Hukuma kamar Sayyid Khamne'i kamar Imamu Ali (as).Daga Zahra Ahmad
Adalci a Hukuma kamar Sayyid Khamne'i kamar Imamu Ali (as).
Daga Zahra Ahmad
Ma'abucin Littafin Tafsirin "Tasneem" Ayatullahi Jawad Amuli Yana cewa:"Wata rana na kasance bako a gidan Sayyid Khamne'i aka kawo mana abinci domin mu ci.Sai dansa Mustapha ya zauna domin ya ci abincin tare da mu,sai Sayyid ya kalle shi ya nemi ya tafi cikin gida ya ci abincin a can,ni know ma sai na nemi ya bar shi mu ci tare.A nan sai Sayyid Qa'id yace da ni:"Wannan abincin an saye shi ne daga dukiyar al'umma,Kai ma bako na ne a kan tattauna lamuran Hukuma da al'umma,hakan ya sa na nemi ta tafi gida ya ci abincin a can."
A nan ne na fahimci dalilin da ya sa Allah ya bai wa wannan bawan Allah izza da daukaka."
Shi ma Imamu Ali (as) wata rana daya daga cikin masu ma'aikatan Gwamnatinsa ya ziyarce shi a gidansa sai ga dansa ya shigo office din,sai aka ga ya KASHE fitila ya kunna Wata ta daban,sad da Dan na shi ya fita sai ya KASHE wannan ya kunna dayar.Sai Sahabin na shi yace da shi:"Ya Imam! na ga kana KASHE fitila kana kunna wata minene dalilili?"Sai Imam Ali (as) yace:"Sad da Dana ya shigo Muna tattauna batun iyalina ne,sai na kashe fitilar Gwamnati na kunna tawa ta kashin-kaina,sad da ya fita sai na kunna fitilar Hukuma na kashe tawa."
Karin haske ma'ana Imam Ali (as) adalcinsa hatta hasken fitilar Hukuma ba ya amfani da shi a kan bukatunsa na kashin kansa.
Wannan adalci dai gidan Annabta (as).
No comments: