labaran kama Syd Khamene'i sau 6 na tsohuwar gwamnatin Shah, da kuma gudun hijirar sa sau 3 kafin Juyin Musulunci na Iran.Daga Bilya Hamza Dass

 labaran kama Syd Khamene'i sau 6 na tsohuwar gwamnatin Shah, da kuma gudun hijirar sa sau 3 kafin Juyin Musulunci na Iran.
Jami'an tsaron kifaffiyar gwamnatin Shah da ake kiran su da SAVAK sun sha kama Syd Khamene'i da wasu abokan shi tare a lokaci daban-daban har sau 6 a tsakanin shekarun 1963 zuwa 1979 saboda ra'ayoyin siyasa da adawa da gwamnatin Shah. 

Ga wasu bayanai game da kama shi:

Kamun farko (1963) An kama Syd Khamene'i a karon farko a shekara ta 1963 shekaru 61 da suka wuce sun zarge shi da sukan gwamnati ta hanyar rubuce-rubuce kan Shah, karkashin jagorancin Ayatullah Ruhollah Khomeini. An kaishi gidan yari an sake shi bayan watanni 5 da kama shi.

Kamu na biyu (1964) An sake kama Syd Khamene'i a shekara ta 1964 saboda ci gaba da gwagwarmaya korar gwamnatin Shah. An kama shi ne a watan 6 wato wata ɗaya kacal bayan ya fito daga wancan kamun. An ɗaure shi tsawon watanni 11.

Kame na uku (1966) A shekarar 1966 an kama Syd Khamene'i tare da daure shi na tsawon watanni 4 saboda rawar da ya taka wajen shirya wata gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnatin Shah. Wacce sama da mutum dubu ɗari 3 suka halatta a wannan lokacin.

Daga nan ne bayan ya fito sai ya bar Mashhad yayi gudun hijira zuwa wani yanki dake ƙarshen Iran a wannan lokacin da ake cewa, 'Iran Shahr' yana karatu, ya zauna a wajan tsawon shekaru 2. Sai a ƙarshen shekarar 1968 Imam Khumaini yayi umurnin ya dawo.

Yana dawowa a 1968 kwana ɗaya bayan ya dawo aka sake kama shi, wanda aka ɗaure shi tsawon watanni 3. Shi ne kamu na 4

Kamu na biyar (1972): An sake kama Syd Khamene'i a 1972 saboda ci gaba da adawa da gwamnatin Shah.


Kame na shida  (1974 da 1976): An sake kama Syd Khamene'i saboda harkokin siyasa da kiran jama'a ga tabbatar da tsarin Muslunci an daure shi na tsawon lokacin.

Bayan ya fito ya sake tafiyar gudun hijira zuwa Birnin Najaf dake Iraƙi ya zauna na ɗan ƙaramin lokaci. A lokacin Imam Khumaini ya bar Najaf ya tafi Faransa yana gudun hijira shi ma.

Bayan nan sai ya dawo, lokaci Tukunyar Juyin Musulunci ta tafasa, sai akayi kokarin ganin bayan shi daga nan ne sai ya sake gudun hijira a karo na 3 daga shekarar (1977-1978) shekarar Syd ya yi hijira zuwa birnin Tabas da ke gabashin kasar Iran, inda ya ci gaba da zama har zuwa juyin juya halin Iran a shekarar 1979. Bayan juyin juya halin Musulunci ya koma Mashhad kuma ya zama babban jigo a  sabuwar gwamnati.

—Bilya Hamza Dass

No comments:

Powered by Blogger.