Dakarun Yemen sun kaddamar da hari a kusa da ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila
Dakarun Yemen sun kaddamar da hari a kusa da ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila
Da sanyin safiyar Juma'a ne wani jirgi maras matuki na dakarun 'yan Shi'a a da ke kasar Yemen, wato Ansarullah Houthi ya samu nasarar kai hari a tsakiyar Tel Aviv, kusa da ofishin jakadancin Amurka, inda harin ya rutsa da yahudawa da dama, kuma a cewar kafofin Labaran Isra'ila, mutum daya ya mutu yayin da aka garzaya da takwas zuwa asibiti.
Isra'ila dai tana da dabi'ar boye ainihin gaskiyar barnar da hare-haren ramuwar gayya da 'yan gwagwarmaya ke kai mata musamman na Falasdinawa, Hezbollah, Yemen da kuma na kasar Iraqi.
Tabbas wannan harin na dakarun Yemen a safiyar Juma'a yana nuni da karfin mayakan Ansarullah domin kuwa na'urorin tsaron Isra'ila da makamanta na tsaron sararin samaniya sun gaza gano cewa jjrgi maras matuki ya kutso har birnin Tel Aviv, ballanta amsa-kuwwa wato siren ya isar da sakon gargadi.
Wannan harin na zuwa ne jim kadan bayan wani mummunan harin ta'addancin da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira Zawayda, Nuseirat da kuma Bureji, inda Falasdinawa 16 suka rasu.
No comments: