WANENE MUHAMMAD DAIFI KWAMANDAN KASSAM-HAMAS DA ISRA'ILA KE NEMA RUWA A JALLO?
WANENE MUHAMMAD DAIFI KWAMANDAN KASSAM-HAMAS DA ISRA'ILA KE NEMA RUWA A JALLO?
A ranar Asabar 13/7/2024 Isra'ila ta Kai wani mummunan hari a yankin Khan-Yunus Wanda ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa 150+ kamar yadda Jaridun cikin gidan Palasdinawa da waje suka rawaito.Wannan harin dai Isra'ila ta Kai shi domin samun bayanan da ta yi na cewa, fitaccen Kwamandan Bataliyar Kassam da mataimakansa na wajen.
Muhammad Daifi dai tun kusan shekara Talatin baya ta shelanta shi a matsayin makiyinta number daya da take nema domin halakar da shi.Bayan Kai harin da 'yan mintuna kafar yada labarai a yayin 12 Channel ta Isra'ila ta bayyana cewa harin ya halaka MUHAMMAD DAIFI da Mataimakinsa Rafi'i Salama.A yayin da 14 Channel Kuma suka bayyana shakkun cewa kila harin ya rutsa da Rafi'i Salama ne a yayin da Muhammad Daifi ya tsallake rijiya da baya.
Muhammad Daifi dai Isra'ila ta ba ta da hotonsa illa guda daya,a waccan shekarar Kuma ta bayyana cewa ta mallaki sabon hotonsa,a yayin da manzarta ke shakku a kan lamarin.A yayin da 13 Channel na Isra'ila ta bayyana cewa dakarunta sun kai mummanan hari a yankin Khan-Yunus din.Jaridar "Yadi'uot-Ahronat" ta rawaito cewa,an yi amfani da manyan Bama-bamai guda 5 Wanda ya lalata duk wani Gini da mutanen da suke ciki Wanda ake tsammani Daifi na ciki.
A yayin da sashen masu kula da labaran Hamas suka musa halaka Muhammad Daifi,a yayin da bayyana cewa, Daifi ba ya muhallin da suka Kai harin ma.
No comments: