ZAMAMN LAFIYA A JIGAWA:GWAMNA NAMADI YA YI ZAMA NA MUSAMMAN DA MASU RUWA DA TSAKI NA JIHAR JIGAWA A KAN ZAMAN LAFIYA DA CI GABAN JIHAR

ZAMAMN LAFIYA A JIGAWA:GWAMNA NAMADI YA YI ZAMA NA MUSAMMAN DA MASU RUWA DA TSAKI NA JIHAR JIGAWA A KAN ZAMAN LAFIYA DA CI GABAN JIHA 
A wannan rana ta Litinin 22/07/2024 mai girma gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA ya yi zama na musamman da masu ruwa da tsaki na jihar Jigawa, wadda su ka haɗa da sarakuna, malamai, jami'an tsaro, ƙungyoyin ƙwadago, ƙungoyoyin Mata, ƙungoyin yan kasuwa, ƙungiyoyin ɗalibai, ƙungiyoyin bakanikai da direbobi, da ƙubgiyar Kiristoci da ƙungiyoyin baƙi mazauna jihar Jigawa da sauransu.

Taron wadda ya gudana a babban ɗakin taro na fadar gwamnati jiha da ke Dutse, an ɗauki tsawon lokaci ana tattaunawa, kan batutuwan da su ka shafi zaman lafiya da cigaba a jihar Jigawa. Tare da kawo shawari kan yadda za a magance matsalolin da ke addabar jama'a a wannan yanayi  da ake ciki.

Mai girma gwamna ya yi jawabi tare da nusar da al'umma dangane da halin da ƙasa ke ciki, da kuma bayyana matsayar gwamnatin jihar Jigawa da irin shirye-shirye da ake domin rage wa al'umma raɗaɗin da ake fama da shi.

Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje, tare da mai martaba sarkin Dutse Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sanusi na daga cikin manyan baƙi masu jawabi a wannan zama. Sun jawo hankalin jama'a a kan muhimmancin zaman lafiya tare da kauce wa duk wani yunƙuri da ka iya barazana da zaman lafiyar al'ummar jihar Jigawa wadda ke da kambun zaman lafiya na tsawon shekaru. Sarakunan biyu sun bayyana irin yadda gwamnatin jihar Jigawa ta buɗe dukkan kofofinta wajen ƙarbar shawara da dukkan ƙorafe-ƙorafe na al'umma.

Kwamahsinan 'yan sanda na jiha, shugaban rundunar soja ta jihar Jigawa, shugaban majalissar malamai ta jiha, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago, shugabannin ɗalibai, ƙungiyar mata ta jihar Jigawa da sauran wakilan matasa, yan kasuwa na daga cikin waɗanda su ka yi jawabi tare da nuna goyon bayan gwamnatin jihar Jigawa a kan irin aikace-aikace na alkhairi da aka sako a gaba. Tare da nesanta kansu da duk wani yunƙuri da wasu ɓata gari ke yi na tayar da hankali da rusa zaman lafiya da tattalin arzikin jihar Jigawa.


Daga ƙarshe, masu ruwa da tsakin na jihar Jigawa, sun yi ƙira ga dukkan al'umma musamman matasa da su guji duk wani shiri da ake na tayar da fitina ko rusa zaman lafiyar Jigawa wadda aka santa da shi. Domin ita fitina idan an san farkonta ba a san ƙarshenta ba, kuma addu'a da komawa ga Allah ita ce babbar mafita ga halin da ake ciki; saboda babu abin da ya fi karfin addu'a ko ya gagari Ubangiji.

Government House Press 
22/7/24.

No comments:

Powered by Blogger.