WATA 9 NA DUFANIL AQSA::SU WANENE MANYAN KWAMANDOJIN HAMAS DA SUKA RIKEWA ISRA'ILA WUYA?Daga Zahra Emaad Ahmad
WATA 9 NA DUFANIL AQSA::SU WANENE MANYAN KWAMANDOJIN HAMAS DA SUKA RIKEWA ISRA'ILA WUYA?
Daga Zahra Emaad Ahmad
Tun ranar Asabat 7 ga Oktobar wannan watan,rundunar gwagwarmaya ta Hamas da ke Palasdinu suka yi martanin kashe wasu Palasdinawa da aka yi ta hanyar kai hari a kan bangarorin tsaro na kasar mamaya wato Isra'ila.
Tun sad da labaran wannan mayar da martani da Palasdinawa suka yi ya fara yaduwa;masanan yaqi da tsaro na kasashe suka fara nazartar yadda Hamas suka kaddamar da harin nan wanda ba a taba yiwa Isra'ila mummunar marna shekaru 70 baya ba kamar shi.Masanan sun ci gaba da nazartar yadda Isra'ila din ta kasance kasa wacce ta ke da tsaro da kuma samun goyon bayan duniya.Amma a gefe guda kuma,an rika tambayar shin wadanne Kwamandoji ne Hamas ta samu da ke jagorantar rundunar zuwa ga wadannan nasarorin,abunda ke tafe bayani ne a kan wadansu Kwamandoji guda 6 da rawar da suka taka wajen kai harin,a sha karatu lafiya.
Muhammad Daifi:Sunansa Muhammad Dayyaf Almisriy an haife shi a shekara ta 1965 a birnin Gazza.Lakabinsa shi ne ''Daifi'' Alkunyarsa ''Abu-Khalid'' Kasar mamaya ta Isra'ila na masa lakabi da ''Mutum daya mai tai 6'' ko ''Aljani wanda ba san fuskarsa ba sai dai ayyukansa'' Ya yi degree dinsa na farko a Jami'ar Musulunci ta Gazza a kan ''Biology'' sannan yana da basirar wasan kwaikwayo da shirya abubuwan da suka shafi ayyukan basira da hazaka.
Sad da aka bayyana Samar da rundubar Hamas a Gazza,ba tare da taradudi da tsoro ba ya tsunduma ciki a shekara ta 1989,sannan Isra'ila ta taba kama shi ta tsare shi na watanni 16 ba tare da an kai shi kotu ba.A sad da yana tsare sun tattauna da Zakariya Shurubarji da da Salah Shahha a kan assasa runduna karkashin Hamas mai suna ''Kassam'' wacce aikinta shirya hare-hare domin kame sojojin mamaya.
A sad aka kama shi an tuhume shi da laifuka daban-daban mafi girma a cikin shi ne shirya harin da ya kai ga mutuwar Yahudawa 50 da raunata da dama a shekarar 1996.Bugu da kari an sake kama shi a shekarar 2000 wanda ya kubuta daga gidan yari bayan wani sulhu da aka yi tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.
Yunkurin halaka shi
Tun sad da aka sake shi a shekarar 2000,bayaninsa,ya buya ga Isra'ila sai dai sun yi yunkurin halaka shi a lokuta mabambanta,amma yana tsallakewa.A shekarar 2002 an kai masa mummunan hari,in da ya kubuta duk da an karya kafarsa da hannunsa kamar yadda Hukumar Isra'ila suka bayyana.Bugu da kari yana fuskantar wahalar magana saboda hare-haren da ya fuskanta a lokuta mabambanta.
A shekarar 2014 Isra'ila ta kaiwa Muhammad Daifi hari sad da ta yi kwanaki 50 tana kaddamar da hare-hare a kan Gazza;sai dai ya tsallake duk da hakan sun kashe matarsa da 'ya'yansa biyu.
A na masa lakabi da ''Daifi'' (ma'ana bako) ne saboda bai da takamaiman wajen rayuwa,bai da takamaiman kayan sawa,rahotanni na bayyana cewa,kusan kullum sai ya canza muhallin da zai kwana saboda batar da sawun MOSSAD yadda take bibiyarsa. Duk hakan har zuwa yanzu Isra'ila ba ta takamaiman hotonsa.
2.Marwan Isa:Shi ne na hannun daman Muhammad Daifi, sannan mataimaki a gare shi kuma abokin gudanar da ayyuka.Isra'ila na masa lakabi da ''sawun Keke'' ba a gane gabanka'' ko kuma ''hawainiya mai caccanzawa''
Isra'ila ta taba kama shi ta tsare har na tsawon shekaru 5 saboda ayyukansa a kungiyar Hamas.
Kungiyar leken asirin Isra'ila ta bayyana shi a matsayin mai juya akalar Hamas,sannan daya daga cikin Jagororinta.Ta bayyana cewa,matukar yana a raye,to tabbas ba za ta yi galaba a kan Hamas ba.
Isra'ila ta yi yunkurin halaka shi a lokuta mabambanta manya a cikinsu su ne a shekarar ''2006,2011,2014,2021''Duk yana tsallakewa sai dai samun raunuka a jikinsa.
Yahaya Sinwar:A watan Yulin 2015 majalissar dinkin duniya ta sanya shi cikin List na 'yan ta'addar kasa-da-kasa.
An haife shi a shekarar 1962 a birnin Gaza.Shi ne yake Jagorantar rundunar ''Majad'' runduna ce ta sirri domin bibiyar motsin MOSSAD da kuma Jagororin Hukumar Isra'ila.
An kama Sinwar sau uku,su ne a shekarar 1988,1982,2011 in da daga lokacin ba a sake kama shi ba.
4.Abdullahi Bargusi:Shi kwararre ne wajen hada Bama-bamai da Nakiyoyi manya da kanana.An haife shi a kasar Kuwaitia shekarar 1972,bayan nan ya sami shaidar zama san kasar Palasdinu.
Bargusi ya zamanto kwararre wajen hada Bama-bamai,shi ne harhada ababen fashewar da suka kai ga mutuwar Isra'ilawa 66,da raunata sama da 500.
An kama shi tattare da kai shi Kotun Isra'ila in da aka yanke masa hukuncin shekaru 65,da Karin shekaru 5200 a tsare.
Bargusi ya yi yajin kin cin abinci da ya kai ga sakinsa bayan wani yunkuri daga rundunar Hamas.A sad da yana tsare ya wallafa littafi mai suna ''AMIRIL-ZIL'' (Ma'ana shugaban inuwa) in da a ciki ya bayyana rayuwarsa da yadda ake hada Bama-bamai da abubuwa masu fashewa.
5 Isma'il Haniyye:Shi ne shugaban sashen siyasa na rundunar Hamas.Ya kasance na hannun daman Shaheed Shaikh Ahmad Yassin da Dr. shaheed Abdul'azeez Rantisiy.
A shekarar 1989 Isra'ila ta tsare shi na shekaru 3,sannan aka kora su iyakar Labnan tare da wasu 'yan Hamas.
6.Kalid Mish'il:Ya kasance cikin wadanda ke kula da sashen siyasa na Hamas.Mutum ne mai basira da hazaka.
Banjamen Natanyahu ya bayar da umarnin bin shi kasar Urdun domin kashe shi ta hanyar amfani da Mambobin MOSSAD;amma ya kubuta bayan Hukumar kasar Urdun sun gano shirin da Isra'ila ke aiwatarwa.
A watan Disambar 2012 ya ziyarci birnin Gazza bayan ya bar kasar tun yana dan shekara 11 da haihuwa.
7.Mahmuod Zahhar:An haifi Zahhar a birnin Gazza a shekarar 1945.Mahaifinsa Dan Palasidinu,Mahaifiyarsa kuma 'yar Misira CE.Ya yi digirinsa na farko a kan harkar lafiya a Jami'ar
''AINISH-SHAMSI'' a kasar Misira a shekarar 1971.
Zahhar dai ya kasance wanda Isra'ila ke kaiwa hare-hare domin kashe shi a lokuta mabambanta amma yana tsira da raunuka.A shekarar 2006 Isra'ila ta wurga Bom a gidansa da niyyar kashe shi wanda nauyinsa zai iya kashe gomomin mutane,amma ya fita da raunuka.
Isra'ila ta kashe babban dansa Khalid a cikin hare-haren da take kaiwa Palasdinawa a Gazza.
Zahhar ya kasance marubuci,manazarci ya rubuta Littafai daban-daban ciki har da wanda ya yiwa Natanyahu raddi.
Wadannan dai sune mutum 7 jiga-jigan kungiyar Hamas da Isra'ila ke nema ta kashe ruwa a jallo.
No comments: