Mayar da martani:Isra'ila ta kai hari kasar Yeman

Mayar da martani:Isra'ila ta kai hari ma'ajiyar man Yeman


Zahra Siddiq


Daya daga cikin manyan kusoshin Gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, Isra'ila ta kai hari kasar Yeman.

Kafar yada labaran "Walah" mai watsa shirye-shiryenta da yaren Ibraniyanci da Isra'ila ta rawaito cewa,ta kai mummunan hari zuwa burning Hadida in da Kai tsaye ya dira a muhalli mallakar  'yan gwagwarmayar Ansarullahi da Yeman.

A wata ruwayar Kuma shafin "Iksus" ya bayyana cewa jiragen Isra'ila sun Kai hari kasar Yeman domin martanin harin da 'yan Hotsi suka Kai birnin TelAviv da ke Isra'ila.

Kafar Talabijin ta kasar Yeman ta bayyana cewa,harin ya dira Kan ma'ajiyar man Fetur din dakarun Ansarullahi in  da Isra'ila ta yi amfani da jirgin Ef-35.

Hukumar lafiyar dakarun Ansarullahi sun bayyana cewa harin ya kashe wasu tare da raunata wasu a birnin Hadeed.

Harin dai mayar da martani ne dangane da harin da Ansarullahi suka Kai birnin TelAviv in da ya yi musu mummunar barna da Asubahin ranar Juma'ar da ta gabata.

No comments:

Powered by Blogger.